in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi bikin murnar cika shekaru 60 da kafuwar jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta
2015-10-01 17:54:02 cri

Yau Alhamis 1 ga watan Oktoba, rana ce ta cika shekaru 66 da kafuwar jamhuriyar jama'ar kasar Sin, kana rana ce ta cika shekaru 60 da kafuwar jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta ta kasar Sin.

Wata tawagar wakilan gwamnatin tsakiyar kasar Sin a karkashin shugabancin Yu Zhengsheng, shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin da wakilai daga sassa daban daban na jihar sun taru a Urumchi, babban birnin jihar domin murnar wannan muhimmiyar rana.

A jawabinsa a wannan biki mai muhimmanci, Yu Zhengsheng ya ce, za a ba muhimmanci ga batun tabbatar da kwanciyar hankali da inganta zamantakewar al'umma yayin da ake gudanar da harkokin tafiyar da jihar ta Xinjiang, kana kuma yanzu za a mai da hankali kan daukar tsauraran matakan yaki da ayyukan nuna karfin tuwo da ayyukan ta'addanci, a kokarin raya jihar ta Xinjiang bisa tsarin gurguzu na musamman, inda sassa daban daban za su hada kai su kuma zauna da juna cikin lumana, kana da samun wadata tare, da ci gaban al'adu, kuma kowa da kowa zai ji dadin zaman rayuwa.

Haka zalika, gwamnatin tsakiyar ta ba da tallafin kudin Sin RMB miliyan 50 domin kara hada kan al'ummomin da ke jihar. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China