Tawagar wakilan gwamnatin kasar Sin ta isa Urumqi don halartar bikin cika shekaru 60 da kafa jihar Xinjiang mai cin gashin kanta ta Uygur
A yau Jumma'a ne wata tawagar da ke kunshe da jami'an hukumomin kasar Sin da ke karkashin jagorancin Yu Zhengsheng, shugaban majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa ta kasa ta isa birnin Urumqi, babban birnin jihar Xinjiang mai cin gashin kanta ta Uygur, domin halartar bukukuwan murnar cika shekaru 60 da kafa jihar. Bayan isar tagawar ta samu maraba da hannu biyu biyu daga al'ummar jihar a filin jirgi.Haka kuma Mr.Yu Zhengsheng shi ne ya jagoranci tawagar halartar bikin mika kyaututuka ga jihar ta Xinjiang inda aka mika ma jihar kyautar girma da shugaban kasar Sin Xi Jingpin ya rubuta cewa gina kyakkyawar Xinjiang, cimma burin kasa tare.
Tawagar mai mambobi 69 zasu halarci kasaitaccen bikin a ranar 1 ga watan gobe na Oktoba.
Xinjiang Uygur mai cin gashin kanta an samar da ita ne a ranar 1ga watan Oktoba na shekara ta 1955 bayan da majalissar dokokin yankin suka zabi gwamnatin farko na yankin.(Lubabatu, Fatimah)