Taken bikin shi ne "Rungumi kasar Sin". Ta hanyar nune-nunen hotuna sama da 700, da kayayyaki sama da 200, har ma da wasu alkaluma da zane-zane, an nuna cewa, a karkashin kulawa daga kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da kuma babbar gudummawa daga jama'a, mutane na kabilu daban daban ta jihar Xinjiang ta kasar Sin sun yi zama tare cikin jituwa, kana sun haye wahalhalu da dama don samu babban ci gaba, musamman ma bayan da aka shirya taron kara-wa-juna-sani karo na 2 game da raya jihar Xinjiang, jihar ta samu babban ci gaba ta fuskokin tattalin arziki, siyasa, al'adu, zamantakewar al'umma, da shugabancin jam'iyyar. (Bako)