A cikin takardar, an ce, tun bayan da aka kafa jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta, jihar ta nace ga bin tsarin cin gashin kanta, gami da aiwatar da manufofin da suka shafi hada kan kabilu yadda ya kamata, kana an kyautata dangantakar dake tsakanin kabilu daban daban bisa tunanin irin na gurguzu cikin daidaito da hadin gwiwa, taimakawar juna, cikin jituwa.
A cikin shekaru 60 da suka gabata, tattalin arzikin jihar Xinjiang ya inganta, wanda ya aza harsashin raya harkokin jihar tare da kyautata zaman rayuwar mazaunan wurin.
San nan, a cikin takardar, an ce, bayan da aka kafa jihar, Xinjiang ta kara inganta harkokin shari'a, tare da nacewa ga yaki da ta'addanci, don sa kaimi ga samun hadin gwiwa cikin daidaito tsakanin kabilu daban daban dake wurin..
Haka kuma, tun bayan da aka kafa sabuwar jamhuriyar kasar Sin, an gudanar da manufar cin gashin kai yadda ya kamata, lamarin da ya taimaka wajen aiwatar da manufar bin addini cikin 'yanci a jihar, kuma, an inganta zaman jituwa tsakanin mabiya mabambantan addini a jihar.
A karshe, takardar ta zayyana cewa, jam'iyyar kwaminis ta Sin da gwamnatin kasar sun dora muhimmanci sosai game da bunkasuwar jihar, da kara karfin taimakawa jihar, matakin da ya taimaka wajen ingiza raya zamantakewar al'umma da tattalin arziki a jihar. (Bako)