in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
GDP na jihar Xinjiang ta Sin ya karu a farkon rabin shekarar bana
2015-07-20 11:22:41 cri
Yawan kudin da jihar Xinjiang mai cin gashin kanta dake kasar Sin ta samu a farkon rabin shekarar da muke ciki, ya karu da kashi 8.2 cikin 100, idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara, inda aka cimma burin kara jawo jari a yankin, da samar da guraben aikin yi, da kara kudin shiga, da kiyaye muhalli. Sakamakon haka, an kyautata tattalin arzikin wannan yanki sosai, kuma an gaggauta yunkurin canja salon bunkasuwar tattalin arzikin yankin.

Bisa labarin da jaridar Xinjiang Daily ta fitar a jiya, an ce mataimakin shugaban hukumar kididdiga ta jihar Wang Yue, ya ce, saurin karuwar GDP ya kai kashi 6.9 cikin 100 a farko watanni 3 na bana, yayin da wannan adadi ya kai kashi 8.2 cikin 100 a farkon rabin shekarar bana. Wannan dai ya nuna irin habakar da aka samu ta fannin tattalin arziki cikin gaggawa. Kaza lika yawan kayayyakin masana'antu da aka sayar ya kai kashi 97.2 cikin 100 a farkon rabin shekarar ta bana, inda aka raya sha'anin masana'antu sosai a jihar.

Kaza lika, kididdigar ta nuna cewa, a wannan shekara ta bana, yawan karuwar GDP da aka samu ta hanyar ba da hidimomi ya kai kashi 58.9 cikin 100, adadin da ya kai fiye da sha'anin kirkire-kirkire, da raya masana'antun jihar. A daya hannun yawan sabbin guraben aikin yi da aka samu a farkon rabin shekarar bana, ya kai dubu 320. Yayin da yawan kudin shiga da mazaunan birane da kauyukan jihar ta Xinjiang suka samu, ya zamo a sahun gaba a kasar Sin. (Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China