A bangon da ke dakin nune-nune, an rataya wani kayan sassaka da ke da mita 1.52, kuma an nuna hoton shugaban Xi, da alamar tambarin jam'iyyar, da tutar kasar Sin da babban filin Tian'anmen da sauransu.
Wadan nan Kawaye guda 2 ne daga gundumar Kuqa ta yankin Aksu ta jihar Xinjiang sun yi wannan kayan sassaka ne da hannu, don yabawa babban canji da aka samu a garinsu bayan da kwamitin tsakiya ya fidda wasu kyawawan manufofi gare su.
Haka kuma, an nuna wasiku da wadannan 'yan mata suka rubuta wa babban sakataren Xi, inda aka nuna cewa, dalilin da ya sa suka iya zaman walwala, sabo da kyawawan manufofin da jam'iyyar da gwamnatin suka bayar, kuma wannan ya nuna kaunar babban sakatare Xi ga jihar Xinjiang, shi ya sa, wadannan 'yan mata sun kashe watanni 2 don sassaka wannan kaya da ke da ma'anar "Hadin gwiwa don cimma burin kasar Sin", kuma sun nuna kyakkyawar fatan su ga kasar Sin tare da godewa babban sakataren Xi.(Bako)




