in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta ciyar da hadin gwiwar kasa da kasa kan aikin tattara kudi gaba
2015-07-16 10:31:41 cri
Wakilin shugaban kasar Sin, kana ministan harkokin kudin kasar ta Sin Lou Jiwei ya bayyana cewa, kasar Sin za ta yi hadin gwiwa tare da bangarorin da abin ya shafa domin inganta hadin gwiwar kasa da kasa kan aikin tattara kudi, ta yadda za a cimma nasarorin samun ci gaba da kuma bunkasuwar tattalin arziki tare.

Ministan ya bayyana haka ne bayan da ya halarci taron tattara kudi na duniya karo na uku da MDD ta kira a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha.

Kaza lika, Lou Jiwei ya jaddada cewa, "yarjejeniyar hada-hadar kudi ta Monterrey" da "sanarwar Doha" sun tabbatar da matsayin hadin gwiwar dake tsakanin kasashe masu tasowa da kasashe masu ci gaba a siyasance, dangane da matakan da ya kamata gamayyar kasa da kasa su bi wajen aiwatar da wadannan yarjejeniyoyi biyu game da karfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasashe masu tasowa da kasashe masu ci gaba.

Ana fatan kasashe masu ci gaba su cika alkawarinsu na samar da taimakon kudade na kashi 0.7 bisa dari na kudin shigarsu ga kasashe masu bukata. A sa'i daya kuma, ya kamata kasashe masu ci gaba su taimaka wa kasashe masu tasowa bisa bukatunsu, su kuma mai da hankali wajen ba su taimako a fannonin da suka shafi kawar da talauci, kiwon lafiya, ba da ilmi, gina kayayyakin more rayuwa da dai sauransu.

Bugu da kari, Lou Jiwei ya bayyana cewa, a matsayinta na kasa mai tasowa mafi girma cikin kasashen duniya, kasar Sin ta kasance mai samun albarka cikin hadin gwiwar bunkasuwa, kana ta kasance mai ba da gudummawa ga wannan aikin. Haka kuma, a matsayinta na mai inganta sabuwar yarjejeniyar hadin gwiwar kasa da kasa wajen neman bunkasuwa, kasar Sin na kokarin kafa bankin zuba jari kan kayayyakin more rayuwar Asiya na AIIB, da kuma sabon bankin raya kasashen BRICS, da dai sauran hukumoin da abin ya shafa.

A sa'i daya kuma, kasar Sin na hada kan kasashen dake kewayen hanyar siliki wajen gudanar da kiran neman bunkasuwa, watau shirin zirin tattalin arziki na siliki da hanyar siliki ta ruwa na karni na 21, kuma kasar Sin na fatan ba da gudummawa yadda ya kamata ga aikin bunkasuwar kasa da kasa, da kuma cimma burin neman ci gaba da bunkasuwar tattalin arziki tare da kasashen duniya. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China