Liu Jieyi ya bayyana cewa, a matakin gaba, kasar Sin za ta samar da taimako ga yankunan da suka taba fama da cutar Ebola bisa bukatunsu, domin samar da goyon baya da kuma halartar ayyukan kafuwar tsarin yin rigakafi kan cututtuka da kuma samar da kayayyakin ba da agaji da kiwon lafiya a nahiyar Afirka, ta yadda za a iya kyautata kwarewar kasashen Afirka wajen fuskantar hadarin kiwon lafiya na gaggawa.
Bugu da kari, Liu Jieyi ya ce, babban tushen farfado da yankunan shi ne ciyar da tattalin arzikin zaman takewar al'umma gaba, ya kamata gamayyar kasa da kasa su ba da taimako ga kasashen yankunan da suka taba fama da cutar Ebola wajen fuskantar hadarurruka daga dukkan fannonin domin tabbatar da dauwamammen ci gaba wadannan kasashe. (Maryam)