Cikin jawabinsa, Mr. Xi ya bayyana cewa, kasar Sin ta yi kira da a gudanar da taron, domin fatan ciyar da hadin gwiwar kasashe masu tasowa gaba, sabo da ko shakka babu, hadin gwiwar kasashe masu tasowa za ta ba da karin gudummawa kan karfafa bunkasuwar kasashen da abin ya shafa da kuma samun dauwamammen ci gaban tattalin arzikin duniya.
Xi Jinping ya sanar da cewa, cikin shekaru biyar masu zuwa, kasar Sin za ta samar da taimako ga kasashe masu tasowa a fannoni guda shida da za su hada da kawar da talauci, yin hadin gwiwa kan ayyukan noma, habaka hadin gwiwar cinikayya, kiyaye muhalli domin fuskantar da sauyin yanayi, kafuwar asibitoci da kuma kafuwar makarantu da cibiyoyin ba da horaswa, ta yadda za a iya taimaka musu wajen raya tattalin arzikinsu da kuma kyautata zaman rayuwar al'ummominsu.
Bugu da kari, cikin shekaru biyar masu zuwa, kasar Sin za ta karbi 'yan kasashe masu tasowa dubu 120 domin su samun horaswa a kasar Sin, da kuma samar da kyautar kudin karatu ga 'yan kasashe masu tasowa dubu 150, haka kuma, za ta ba da horaswa ga kwararru na kasashe masu tasowa dubu dari 5. Sa'an nan kuma, kasar Sin za ta kafa kwalejin bunkasa hadin gwiwar kasashe masu tasowa, da kuma samar da hukumar kiwon lafiya ta duniya ta WHO taimakon kudi na dallar Amurka miliyan 2.
Kaza lika, Xi Jinping ya jaddada cewa, kasar Sin za ta hada bunkasuwar kanta da bunkasuwar kasashe masu tasowa tare, ta yadda za mu samu cigaba cikin hadin gwiwa. (Maryam)