in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin tare da uwargidansa sun halarci liyafar da shugaban kasar Amurka ya shirya musu
2015-09-26 17:51:33 cri

A jiya Jumma'a da dare, shugaban kasar Sin Xi Jinping tare da uwargidansa Peng Liyuan suka halarci liyafar maraba da shugaban kasar Amurka Barack Obama ya shirya musu a fadar White House.

A jawabin da ya gabatar wurin liyafar, shugaba Obama ya ce, Shi da shugaba Xi Jinping sun cimma matsaya game da ci gaba da inganta hadin gwiwar kasashen biyu ta fannoni daban daban. Yace ba ma kawai don Amurka da Sin na bukatar hadin gwiwa da juna ba, haka kuma suna iya tabbatar da hadin gwiwar, saboda zumuncin da ke tsakanin jama'ar kasashen biyu ya ba su kwarin gwiwa.

Daga nasa bangaren, Mr.Xi Jinping ya jaddada cewa, a cikin shekaru sama da 30 da suka wuce, Sin da Amurka sun cimma nasarori a cigaban huldar da ke tsakaninsu, kuma ana da imanin cewa, kasashen biyu za su rungumi kyakkyawar makomar huldarsu.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China