Shugaba kasar Sin Xi Jinping ya jaddada a ranar Asabar 26 ga wata cewa, kasashe masu tasowa na hada kansu ne cikin adalci kuma ba tare da boye kome ba.
Shugaba Xi ya fadi hakan ne a yayin da ya halarci tare da jagorantar taron yin hadin gwiwa a tsakanin kasashe masu tasowa, wanda kasar Sin da MDD suka shirya tare a babban zauren MDD da ke birnin New York na kasar Amurka. Ya kuma bayyana cewa, a fannin siyasa, kasar Sin na tsayawa tsayin daka kan bin ka'idoji 5 na yin zaman tare cikin lumana da kuma wasu muhimman ka'idojin raya huldar da ke tsakanin kasa da kasa, kasar Sin na yin cudanya da kasashen duniya cikin adalci kome girmanta. Ba ta tsoma baki cikin harkokin cikin gida nasu. Tana girmama hanyar raya kasa da kuma tsarin zamantakewar al'ummar kasa da kasashen duniya suka zaba da kansu. A fannin tattalin arziki kuma, kasar Sin na girmama bukatun saura. Ba ta gindaya wasu sharadan siyasa ba.
Hadin gwiwar da ke tsakanin kasashe masu tasowa, hadin gwiwa ce da ake yi domin neman samun moriyar juna da nasara tare. Kasashe masu tasowa na cudanya da juna, suna taimakawa juna, suna kokarin raya kasuwannin duniya cikin hadin gwiwa. Har wa yau, hadin gwiwar da ke tsakanin kasashe masu tasowa, hadin gwiwa ce da ake yi domin hada kai da taimakawa juna. Suna kiyaye adalci a duniya, suna kare halaltattun hakkokinsu, suna taka muhimmiyar rawa wajen kiyaye zaman lafiya a duniya da kuma kara azama kan samun ci gaba tare. (Tasallah)