in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya isa birnin Newyork don halartar taron MDD
2015-09-26 17:19:53 cri
A safiyar Asabar din nan shugaban kasar Sin ya isa birnin New York domin halartar taron koli da za'a yi don bikin cika shekaru 70 da kafa MDD.

A lokacin ziyarar aikin da zai yi a Newyork shugaban na Sin zai shiga cikin jerin tarurruka na majalissar da ya kunshi shirin muradan karni bayan shekara ta 2015, ayyukan cigaban mata, hadin kan kasashe masu tasowa daga cikin sauran su.

Shugaban na Sin zai kuma yi jawabi a karon farko a zauren majalissar a cikin wani gaggarumar mahawara da zai bayyana ra'ayin Sin game da inganta zaman lafiya da cigaba tare da tattauna kalubalolin da ake fuskanta a duniyar yau.

Har ila yau ana sa ran zai yi tattaunawar hadin gwiwwa da sauran shugabannin kasashen duniya duk a wani bangare na taron majalissar.

Shugaban na kasar Sin wanda ya isa birnin New York bisa gayyatar da babban magatakardar MDD Ban Ki-Moon ya mika mashi ya fara yada zango a birnin Washington DC bayan kamala ziyarar shi a birnin Seattle wanda shi ne zangon shi na farko duk a ziyarar da yake yi a kasar Amurka.(Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China