"Ina matukar nuna godiya da wannan muhimmiyyar kyauta da wannan niyya taku mai karfi. Wannan wani tunani ne mai cike da haske", in ji sakatare janar na MDD, Ban Ki-moon, dake shugabantar zaman taro na manyan jami'ai kan dangantaka tsakanin kasashe masu tasowa.
Duk a wannan rana, shugaban Sin Xi Jinping ya ba da sanarwa a yayin babban taron MDD kan ci gaba mai karko cewa Sin za ta tattara dalar Amurka biliyan biyu domin bunkasa irin wannan dangantaka.
Takwaransa na kasar Afrika ta Kudu, Jacob Zuma, dake shugabantar gungun 77 a wannan karon, ya nuna godiya sosai ga shugaba Xi game da wadannan shawarwari masu ma'ana da tasiri, a yayin da ita kuma shugabar gwamnatin Bangladesh Sheika Hasina ta kimanta su a matsayin shawarwari masu nagarta.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewa wannan dandali yana da muhimmancin gaske. A cewarsa, yana wakiltar wata dama ta yin musanyar ra'ayoyi kan yadda za a karfafa dangantaka tsakanin kasashe masu tasowa bisa tsarin aiwatar da shirin bunkasuwa na bayan shekarar 2015. (Maman Ada)