in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin tayi alkawarin kudin dala biliyan uku ga kasashe masu tasowa domin yaki da sauyin yanayi
2015-09-26 17:49:30 cri
Kasar Sin a ranar jumma'a ta yi alkwarin bada kudi yuan biliyan 20 kwatankwacin dala biliyan 3 domin taimaka ma kasashe maso tasowa yaki da sauyin yanayi.

Asusun kasar na hadin kan kasashe masu tasowa wajen tinkarar sauyin yanayi zai kuma inganta karfin su ta yadda zasu amfana daga asusun kamar yadda aka sanya hannu cikin sanarwar shugaba akan sauyin yanayi a lokacin ziyarar shugaban kasar Sin Xi Jinping a Amurkan.

Sin da Amurka sun fahimci muhimmancin taimakawa wajen samar da kudade da zai bada damar samar da ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba a kasashe maso tasowa musamman kasashen da suke baya sosai a cigaba,kasashen dake tasowa na kananan tsibirai da kuma kasashen Afrika a cewar sanarwar.(Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China