in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya gana da Ban Ki-moon
2015-09-27 10:01:58 cri

A ranar Asabar 26 ga watan, shugaban kasar Sin Xi Jinping wanda yake ziyara hedkwatar MDD dake New York, ya gana da Mr. Ban Ki-moon, babban sakataren MDD.

A yayin ganawar, Xi Jinpng ya nuna cewa, wannan ne karo na farko da ya kawo ziyara a nan hedkwatar MDD. Shugabannin kasashen duniya suna taro a cibiyar MDD dake New York, wannan ya bayyana sosai cewa, kusan dukkan kasashe mambobin MDD na nuna goyon baya da kuma jaddada fatansu ga MDD na ganin ta ci gaba da taka karin rawa kan batutuwan kasa da kasa. Ya kamata kasashen duniya su yi amfani da damar taya murnar cika shekaru 70 na karfuwar MDD, domin su tsaya kan matsayin bin hanyar sa kaimi ga bangarori daban daban da su taka rawa tare domin kare ruhu da ka'idodin tsarin mulkin MDD da ikonta da rawar da take takawa, ta yadda za a iya kiyaye zaman lafiya da neman samun bunkasuwar duniya baki daya.

Xi Jinping ya jaddada cewa, bangarori daban daban suna fatan a cikin shekaru 10 masu zuwa, MDD za ta ci gaba da tsayawa kan matsayinta na warware matsaloli masu jawo hankulan mutane a siyasance. Ya kamata MDD da kwamitin sulhunta su yi koyi da kyawawan fasahohin da aka samu daga lamarin daidaita batun nukiliya na Iran, wato a tsaya kan matsayin bin hanyar warware batun ta hanyar yin shawarwari.

Sannan Xi Jinping ya ce, ya kamata kasashe masu arziki su sauke nauyin tarihi da aka dora musu na tallafawa kasashe masu tasowa a fannonin kudi da fasahohin zamani. Mr. Xi yana kuma fatan MDD za ta bayar da gudummawar jagoranta kan batutuwan da ke shafar duniya baki daya. MDD wani dandali ne mafi kyau da kasashen duniya za su iya yin amfani da shi wajen yin hadin gwiwar yakar ta'addanci. Ya kamata kasashe mambobin MDD su tafiyar da kuduran kwamitin sulhun MDD da babban shirin yakar ta'addanci da aka zartas a yayin babban taron MDD domin dakile ta'addanci ta hanyoyi iri daban daban.

Bugu da kari, Mr. Xi ya kara da cewa, kasar Sin ta ba da shawarar kafa wata sabuwar dangantakar kasa da kasa irin ta yin hadin gwiwa da neman nasara tare, kuma za ta ci gaba da tsayawa tsayin daka kan matsayin neman ci gaba cikin lumana, har ma za ta kara yin kokarin tsaron odar kasa da kasa da ake bi yanzu bisa kundin mulkin MDD. Mr. Xi ya alkawarta cewa, kasar Sin za ta ci gaba da nuna goyon baya ga MDD da karfafa hadin gwiwa tsakaninta da MDD.

A nasa bangaren, Mr. Ban Ki-moon ya sake maraba da ziyarar farko ta Xi Jinping a MDD bayan ya hau kan mukamin shugaban kasar Sin. Ban Ki-moon ya kara da cewa, kasar Sin muhimmiyar mamba ce ta kasashen duniya, kuma muhimmiyar abokiya ce ta MDD da ake fatan kasancewarta a kullum. Kasar Sin ta dade tana taka kyakkyawar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya da neman bunkasuwar duniya gaba daya, kuma ta bayar da muhimmiyar gudummawarta wajen warware matsalolin kasa da kasa da na shiyya-shiyya kamar yadda ya kamata. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China