150924-An-bukaci-babban-sakataren-hukumar-FIFA-ya-yi-murabus-zainab.m4a
|
Sanarwar ta bayyana cewa, hukumar FIFA ta gano wasu zarge-zarge da ake yiwa Valcke, don haka ta bukaci kwamitinta na kula da da'ar ma'aikata da ya gudanar da bincike a kan sa.
Jérôme Valcke mai shekaru 54 da haihuwa, ya zama babban sakataren hukumar FIFA a shekarar 2007. Yayin da ake bincike kan zarge-zargen cin hanci a hukumar ta FIFA, an zarge shi da karbar kudi har dala miliyan 10 daga kasar Afirka ta Kudu, kana ya saka a asusun ajiyar Jack Warner a shekarar 2008, wanda a lokacin ya ke kan kujerar shugaban hukumar wasan kwallon kafa ta yankin Arewacin Amurka da tsakiya, da kuma yankin Caribbean .
A ganin hukumar shari'a ta kasar Amurka,an ba da wadannan kudi ne a toshiyar baki, domin a baiwa kasar Afirka ta Kudun damar karbar bakuncin gasar cin kofin duniya da ya gudana a shekarar 2010.
Soke mukamin Valcke da FIFA ta yi, wani mataki ne na fara yaki da cin hanci a hukumar FIFA. Don haka, a ranar 18 ga wata, Sepp Blatter ya bayyana fatansa cewar ya kamata a hada kai a cikin hukumar FIFA don warware matsaloli tare.
A wannan rana, Sepp Blatter ya aike da sakon E-mail ga ma'aikatan hukumar FIFA fiye da dari hudu, inda ya bayyana cewa, ya yi imani cewa, FIFA za ta warware matsalolin da ta ke fuskanta tare da sake dawo da mutuncinta don ci gaba da bunkasa sha'anin wasan kwallon kafa a duniya. Don haka, yana fatan dukkan ma'aikatan hukumar FIFA za su ci gaba da kokari a kan ayyukansu.(Zainab)