150813-Neymar-ba-zai-buga-Super-Cup-ba-zainab.m4a
|
Wata majiya ta kulaf din na Barcelona, ta bayyana cewa yanzu haka an yiwa Neymar riga kafin wata cuta ta kumburin makoshi da yake fama da ita, ya kuma koma kulaf din na sa cikin kuzari bayan kammala hutu. Sai dai yanayin jikin sa a cewar majiyar ba zai bashi damar taka leda nan da dan lokaci ba, lamarin da ya sanya ake ganin ba zai buga wasan Europa Super Cup da na Sifaniya Super Cup wanda za a buga a ranekun 14 da 17 ga watan nan ba, da ma wasannin bude gasar La Liga a ranar 22 ga watan nan na Agusta.
Ana dai sa ran Neymar zai yi hutun akalla kwanaki 15 kafin ya koma taka leda.
Neymar wanda ya fara bugawa Barcelona kwallo a kakar shekarar 2013, ya dan samu rashin lafiya a farkon zuwan sa kulaf din. Kana a shekarar da ta gabata ma ya samu rauni a kashin bayan sa, yayin gasar cin kofin duniya da aka buga a Brazil. Wannan karo shi ne na uku da dan wasan ke fuskantar rashin lafiya gabanin bude sabuwar kakar wasanni.
An ce mai yiwuwa kocin Barcelona Luis Enrique, ya maye gurbin Neymar da Pedro Rodriguez a wasannin da kungiyar za ta buga na kwana kwanan nan, duk da cewa shi ma Rodriguez din na shirin sauya sheka zuwa Manchester United. (Saminu Alhassan)