Kungiyar ta 'yan kasa da shekaru 20, a cewar kocin ta Peter Dedevbo, za ta fara atisaye a ranar Lahadin karshen makon nan, gabanin wasan ta na gaba, kuma na biyu a share fagen buga gasar cin kofin duniya ajin mata matasa.
Da yake karin haske game da hakan, koci Dedevbo ya ce dukkanin 'yan wasan kungiyar su 30 sun riga sun taru a sansanin horaswa. Za kuma su yi duk mai yiwuwa domin tabbatar da sun lashe wasan dake tafe.
A baya dai kungiyar ta Najeriya ta samu nasara kan takwarar ta ta Liberia da kwallaye 14 da 1, a wasannin da suka buga a zagayen wasannin na farko cikin watan Yulin da ya shude.
Bayan wasan na Najeriya da janhuriyar dimokaradiyyar Congo, kasar da ta samu nasara za ta kara da ko dai Zambia, ko kuma Afirka ta Kudu. Kana a karshen zagayen wasannin, kasashe biyu da suka zamo a sahun gaba, za su wakilci nahiyar Afirka a gasar cin kofin duniya na shekarar badi, wanda za a buga a Papua New Guinea dake yankin kasashen Oceania.
A bara kungiyar Najeriya ce ta zamo ta biyu a gasar ta cin kofin duniya karo na 7 da kasar Jamus ta samu nasarar lashewa, wadda kuma ta gudana a kasar Canada.(Saminu Alhassan)