in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ronaldo ya kafa tarihi a Madrid yayin da Barca ke ci gaba da rike matsayin ta a saman teburin La liga
2015-09-17 13:24:56 cri

Shahararren dan wasan kungiyar Real Madrid Cristiano Ronaldo, ya kafa tarihin kasancewa dan wasa da yafi kowa ciwa kungiyar kwallaye, bayan da ya zura kwallaye 5 a ragar Espanyol, a wasan ranar Asabar din karshen mako wanda kungiyoyin biyu suka tashi 6 da nema.

Dan wansan dan kasar Portugal wanda ya samu tallafi daga Gareth Bale da Karim Benzema, ya bude ragar Espaniyol ne cikin mintuna 7 da fara wasa, kafin kuma ya kara kwallaye 4. Kwallon ta 6 Karim Benzema ne ya zura ta, wanda hakan ke nuna cewa Real Madrid ta ci kwallaye 11 a wasannin La Liga 2 da ta buga a baya bayan nan.

A daya hannun kuma Leo Messi ya ciwa kungiyar sa ta Barcelona kwallo daya, a wasan da suka kara da Atletico Madrid a filin wasan na Vicente Calderon a ranar Asabar. A kuma gabar da yake murnar samun karuwa ta haihuwa dan sa na biyu. Da fari dai dan wasan Atletico Fernando Torres ne ya fara jefa kwallo a ragar Barca, jim kadan da dawowa hutun rabin lokaci, sai kuma kwallon Neymar ta bugun free kick. Kafin kuma Messi ya jefa kwallo ta biyu a ragar Atletico wadda ta zamo raba gardama.

Sauran wasannin da aka buga a gasar ta La Liga sun hada da wasan ranar

Juma'a 11 ga wata, inda Levante ta tashi wasa da Sevilla kunnen doki 1 da 1.

Sai kuma ranar Asabar, inda Valencia ta lashe wasan ta da Sporting Gijon 1 da nema. A dai Asabar din an buga wasa tsakanin Betis da Real Sociedad, wanda Betis din ta lashe da ci 1-0.

Sai kuma wasan Villlarreal da Granada a ranar Lahadi, wasan da aka tashi Villarreal na da ci 3 Granada na da kwallo 1. Akwai kuma wasa tsakanin Athletic Bilbao da Getafe, wanda aka tashi Bilbao na da 2 Getafe na da kwallo daya. Dan wasan Bilbao Aritz Aduriz ne ya fara jefawa kungiyar sa kwallo ta farko, kafin kuma sabon dan wasan kungiyar Raul Garcia ya kara ta biyu. An tashi wasan na wannan rana 2 da 1 bayan da Aduriz na Getafe ya jefa kwallo daya a ragar Bilbao ana saura mintuna 15 a hura tashi.

Sai kuma wasan Celta Vigo da Las Palmas wanda suka tashi kunnen doki 3 da 3. Haka ma wasan Malaga da Eibar, wanda kungiyoyin biyu suka tashi kunne doki ba ci. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China