in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Super Eagles ta kira 'yan wasa 18 a shirin ta na samun gurbin gasar AFCON
2015-08-19 16:03:24 cri
Sabon kocin kungiyar kwallon kafar Najeriya Sunday Oliseh, ya fidda sunayen 'yan wasa 18 masu buga kwallo a kasashen waje, wadanda aka gayyato domin bugawa kasar wasannin share fagen shiga gasar cin kofin kwallon kafar nahiyar Afirka dake tafe a shekara ta 2017 a kasar Gabon.

Najeriyar dai za ta buga wasan ta na gaba ne da kasar Tanzania, a ranar 4 ga watan Satumbar dake tafe a birnin Dar es Salaam na kasar ta Tanzaniya.

Rahotanni sun nuna cewa kocin ya zabi Vincent Enyeama, a matsayin mai tsaron gida na farko kuma keftin din kungiyar ta Super Eagles. Sai kuma sauran 'yan wasa irin su masu tsaron baya Godfrey Oboabona, da Leon Balogun da kuma Kenneth Omeruo.

A tsakiyar fili kuwa akwai irin su Rabiu Ibrahim, da Lukman Haruna da Joel Obi, da kuma 'yan gaba kamar Ahmed Musa, da Emmanuel Emenike da Anthony Ujah.

Masu nazartar kungiyar sun ce akwai 'yan wasa da aka yi mamakin ganin sunayen su a wannan jadawali na koci Oliseh, wadanda suka hada da mai tsaron gida Carl Ikeme, da dan wasan tsakiya Ernest Uzochukwu, da 'yan wasan gaba Emem Eduok, da Sylvester Igboun da kuma Moses Simon.

An ce ana fatan daukacin 'yan wasan 18 za su hallara a birnin Abuja nan da 31 ga watan nan na Agusta, inda za su hadu da sauran 'yan wasa na gida su 23, gabanin bude atisayen.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China