in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Rasha ya halarci bikin wala-walar gasar cin kofin duniya ta shekarar 2018
2015-07-30 09:54:38 cri

A daren ranar Asabar ne aka gudanar da bikin wala-walar raba rukunonin gasar cin kofin duniya ta shekarar 2018, a fadar Konstantin dake birnin St.Petersburg na kasar Rasha, bikin da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin, da shugaban hukumar FIFA Sepp Blatter suka halar ta.

A cikin jawabinsa, Putin ya yi alkawari cewa kasar Rasha za ta kammala ayyukan shirya gasar cin kofin duniya na shekarar 2018 yadda ya kamata. Putin ya ce, gudanar da gasar cin kofin duniya yana sahun gaba cikin manyan abubuwan da Rasha ke maida muhimmanci a kan sa. Kana hakan zai samar da kyakkyawar damar nuna matsayin kasar Rasha game da bude kofa, da hakurin ta da juriya a tsakanin kasashen duniya.

Putin ya kara da cewa, zabar kasar Rasha a matsayin mai masaukin bakin gasar cin kofin duniya na shekarar 2018, zai kara yada manufar wasan kwallon kafa a fadin duniya. A ganinsa, wannan ce ka'idar da membobin hukumar FIFA suke bi wajen zabar wuri da zai dau bakuncin gasar ta shekarar 2018. Kaza lika hakan ya sawa Rasha kaimi, da ma kasashen dake makwabtaka da ita wajen kara nuna sha'awa ga wasan kwallon kafa.

Shugaba Putin ya kara da cewa, za a gudanar da wasannin gasar cin kofin duniya na shekarar 2018 a birane 11 na kasar Rasha, wadanda suke da al'adu da tarihin musamman a kasar. Kuma kasar Rasha za ta yi kokarin samar da kyakkyawan yanayi ga dukkan kungiyoyi masu halartar gasar, da kuma masu sha'awar kwallon kafa.

A nasa bangare shugaban hukumar FIFA Blatter ya yi jawabin a gun bikin, inda ya nuna goyon bayan sa ga kasar Rasha, game burin ta na karbar bakuncin gasar cin kofin duniya na shekarar 2018. Ya ce hukumar FIFA za ta samar da gudummawa da goyon baya ga kasar Rasha.

An ce, bayan gabatar da sakamakon wala-walar, kungiyoyi 180 za su buga wasanni, domin neman shiga gasar, tare da kasar Rasha wadda za ta zamo mai masaukin bakin gasar.

Za a gudanar da gasar ne a ranar 14 ga watan Yuni na shekarar 2018, za kuma a buga wasa na farko a filin wasa na Luzhniki dake birnin Moscow.(Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China