in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dan bayan Barcelona Vermaelen ya sake jin rauni
2015-09-17 13:23:35 cri
Dan bayan Barcelona Vermaelen ya sake jin rauni

Dan bayan kungiyar Barcelona Thomas Vermaelen, ya sake samun rauni a kafa, yayin wasan daren ranar Asabar, lokacin da kungiyar sa ta doke Atletico Madrid da ci 2-1.

Vermaelen dai ya fice daga wasan ne mintuna 25 da take kwallo, kafin hakan ya maye gurbin Gerard Pique, wanda aka kakabawa takunkumin hana buga wasanni biyu. Ba a dai kai ga bayyana tsahon lokacin da dan wasan zai shafe yana jiyya ba. koda yake ana hasashen mai yiwuwa ya kwashe makwanni 3 ko fiye. Dan wasan dai ya sha fama da matsalar kwanji a kafar sa cikin shekaru ukun baya bayan na. Shi ma dan wasan kungiyar Dani Alves na shan fama da makamanciyar wannan matsala, don haka ake ganin ya zama tilas Marc Bartra ya rike bayan kungiyar, a wasannin da Barca zata buga karshen wannan sati.

Gabriel na fatan komawa Barcelona

Dan wasan gaban Santos Gabriel Barbosa, ya ce yana fatan taka leda a Barcelona idan har kungiyar ta amince ta dauke shi. Barbosa dan shekaru 19 da haihuwa, na cikin 'yan wasan Santos 3 da Barcelonan ta nuna sha'awar daukar su lokacin da ta kulla kwagilar da Neymar a shekarar 2013.

Da yake tsokaci game da hakan, Barbosa ya ce babban burin sa ne ya taka leda a Barcelona, musamman tare da taurarin kungiyar kamar Messi da Neymar wadanda yake matukar girmamawa. Ya ce daukacin 'yan wasa kwallon kafa na mafarkin taka leda a Barcelona, kuma shi ma bashi da banbanci da sauran 'yan wasa a wannan fage.

Yanzu haka dai Barbosa ya bugawa Santos wasanni 39, ya kuma ciwa kungiyar kwallaye 12. A baya kuma ana danganta wasu kulaflika kamar su Manchester United, da Real Madrid da Inter Milan da nuna bukatar daukar wannan dan wasa dan asalin kasar Brazil.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China