Ya kuma kara da cewa, wannan zai kasance karo na farko da Xi Jinping ya kawo ziyara a MDD a matsayin shugaban kasar Sin, kuma a wannan muhimmin lokaci, shugaba Xi Jinping zai hadu da manyan shugabannin kasa da kasa, inda za su tattauna shirin neman dauwamammen ci gaban duniya dake shafar harkokin kawar da talauci, kiyaya muhalli da kuma zaman rayuwar bil Adama.
Kana ya ce, a matsayinta na zaunannen kwamitin sulhu na MDD, kasar Sin ta ba da babbar gudummawa wajen kiyaye zaman lafiya da tsaron kasa da kasa da kuma kawar da talauci, yana fatan kasar Sin za ta iya ci gaba da ba da jagoranci kan ayyukan fuskantar kalubalolin duniya, haka kuma, MDD tana son yin hadin gwiwa da gwamnati da jama'ar kasar Sin wajen cimma burinmu na samun dauwamammen ci gaba.
Bugu da kari, Ban Ki-moon ya nuna yabo matuka kan shirin zirin tattalin arziki na siliki da hanyar siliki ta ruwa na karni na 21 da na kafa bankin zuba jari kan kayayyakin more rayuwa na Asiya da kasar Sin ta gabatar, ya kuma bayyana cewa, MDD za ta dukufa wajen yin hadin gwiwa da kasar Sin a fannin. (Maryam)