in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya fara ziyarar aiki a kasar Amurka a hukunce
2015-09-23 08:58:48 cri

A jiya Talata da misalin karfe karfe 9 da rabi na safe agogon wurin shugaban kasar Sin Xi Jinping ya isa birnin Seattle dake jihar Washington ta kasar Amurka,don fara ziyarar aikin da ya kai kasar Amurka a hukunce.

Shugaba Xi ya yi nuni da cewa, makasudin ziyararsa a kasar Amurka shi ne, don inganta dankon zumunci da ke tsakanin jama'ar kasashen biyu, da karfafa hakikanin hadin gwiwa a fannoni daban daban, da ingiza sabon nau'in dangantakar Sin da Amurka zuwa gaba. Ana kuma sa ran zai yi musayar ra'ayi tare da takwaransa na kasar Amurka Barack Obama game da dangantakar bangarorin biyu da ma halin da kasashen duniya ke ciki, da ganawa da bangarorin al'umma daban daban na Amurka, don ci gaba da tattauna babbar manufar raya dangantakar bangarorin biyu.

Seattle ya kasance zango na farko a ziyarar da shugaban kasar Sin ya fara kasar Amurka, daga bisani kuma, zai ziyarci birnin Washington D.C, da halartar taron koli na zagayowar cika shekaru 70 da kafa M.D.D. a birnin New York.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China