in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya jaddada cewa, aikin samun ci gaba ya zama babban aiki dake gaban kasar
2015-09-23 10:47:15 cri

Shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya bayyana a yayin da ya halarci liyafar da gwamnatin jihar Washington da kungiyoyin sada zumunta na Amurka suka shirya don maraba da zuwansa kasar Amurka a ranar 22 ga wata, cewar aikin samun ci gaba shi ne muhimmin aikin da kasar Sin ta sanya a gaba.

Shugaba Xi ya ce, za a raya tattalin arziki da kyau kuma cikin hanzari. Sin za ta dauki matakan da suka dace don tabbatar da karuwar tattalin arzikin kasar, da sa kaimi ga yin kwaskwarima da canja salon neman bunkasuwa, da kawo alheri ga jama'a da tinkarar barazana don sa kaimi ga raya tattalin arziki cikin sauri.

Haka kuma, Sin ta nace ga bin manufar bude kofa ga kasashen waje da yin gyare-gyare a cikin gida, da bin dokoki, da dage wa kan hanyar samun bunkasuwa cikin lumana. Za kuma ta yi kokari tare da kasashen duniya, don kulla dangantakar hadin gwiwa da samun moriyar juna tsakanin Sin da Amurka. Ya zama wajibi kasashen Sin da Amurka su nace ga raya sabon nau'in dangantakar bangarorin biyu, da nazarin manyan tsare-tsare na kasashensu, don tashi tsaye wajen karfafa hadin gwiwa, da kawar da sabanin da ke tsakaninsu cikin ruwan sanyi, da sada zumunci tsakanin al'ummomin kasashen, ta hakan dangantakar za ta samu makoma mai haske.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China