Tattaunawar da shugaban kasar Sin ya yi da jaridar Wall Street Journal ta samu karbuwa
Kafin ziyararsa zuwa kasar Amurka, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya tattauna tare da jaridar Wall Street Journal ta kasar Amurka, inda ya amsa tambayoyin da aka yi masa dangane da huldar da ke tsakanin Sin da Amurka da kyautata tsarin kula wa da harkokin duniya da hadin gwiwar kasashen biyu kan harkokin Asiya da fasifik da na duniya baki daya da kuma jarin da kamfanonin ketare ke zubawa a kasar Sin da yanayin tattalin arzikin duniya da inganta gyare-gyare daga dukkan fannoni.
Bayanan da shugaban ya yi kan batutuwan sun kuma samu karbuwa daga kasa da kasa, inda wasu masana suke ganin cewa, bayanan sun karfafa gwiwar kasa da kasa kan bunkasuwar kasar Sin.(Lubabatu)