Kakakin babban sakataren MDD Stephane Dujarric ya bayyana a jiya cewa, MDD ta farin ciki da ziyarar da shugaban kasar Sin Xi Jinping zai kai a MDD, ana kuma sa ran babban sakataren MDD Ban Ki-moon zai tattauna wasu manyan batutuwa da shugaba Xi Jinping. Kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa kan muhimman batutuwa kamar batun ci gaba mai dorewa, kawar da talauci, da sauyin yanayi da sauransu.
Bisa gayyatar da babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya yi masa, shugaban kasar Sin Xi Jinping zai je hedkwatar MDD da ke birnin New York tare da halartar tarukan cika shekaru 70 da kafuwar MDD daga ranar 26 zuwa 28 ga wata. (Zainab)