in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Sin ya ba da tabbaci ga 'yan kasuwan Amurka game da tattalin arziki
2015-09-24 09:31:48 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping a ranar Laraban nan ya ba da tabbaci ga shugabannin 'yan kasuwa na Amurka a kan matukar karfin tattalin arzikin Sin tare da yin kira da a karfafa dangantaka na moriyar juna tsakanin kasashen biyu.

Shugaba Xi wanda ya bayyana hakan a zaman tattaunawa tsakanin manyan shugabannin 'yan kasuwa na Sin da Amurka a birnin Seattle a yayin ziyarar aiki ta kwana ta biyu da zai yi a mako daya a Amurka ya ce, yadda tattalin arzikin kasar Sin ke tunkarar ci gaba da fadada ba zai canza ba.

Ya gaya wa manyan 'yan kasuwan bangarorin biyu sama da 30, daga cikin su akwai shugabannin kamfanonin Alibaba, Lenovo, IBM da Microsoft cewa, ginshikin tattalin arzikin kasar Sin har yanzu yana da karfin shi, kuma zai ci gaba da zama a haka cikin dogon lokaci, yana tafiya a tsanake daga matsakaici zuwa babban matsayi.

Mr Xi Jinping har ila yau ya lura da cewa, akwai wassu sabbin dama da kasashen biyu ke fuskanta, don haka ya yi kira da a kara zurfafa hadin gwiwwa wajen kasuwanci tsakanin juna wanda zai habaka ci gabansu da na duniya baki daya.

Ya ce, gwamnatin kasar Sin na goyon bayan manyan kamfanonin Amurka su kafa cibiyoyin kasuwancinsu na yanki, ko cibiyoyin bincike a kasar Sin. Har ila yau tana ba da kwarin gwiwwa ga karin kanana da matsakaitan kamfanoni da su habaka kasuwancinsu a Sin.

A wani bangaren kuma, in ji shugaba Xi, Sin za ta kara adadin zuba jarinta a Amurka. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China