Shugaba Xi ya yi na'am da taron tattaunawar na wannan karo da ya daba muhimmanci sosai game da raya tattalin arziki ba tare da gurbata muhalli ba, kuma ya bayyana cewar wannan ya dace da yanayin da kasashen biyu ke ciki, da ma kalubalen da ake fuskanta a duk duniya. Shugaba Xi ya jaddada cewa, a halin yanzu an zurfafa aikin dunkulewar tattalin arzikin duniya baki daya, kana Sin da Amurka sun karfafa hadin gwiwa a tsakaninsu. Ya kara da cewa akwai makoma mai kyau na yin mu'amala a tsakanin bangarori daban daban na kasashen biyu. Sannan ya ce ya zama wajibi bangarorin biyu sun yi amfani da babbar dama da tattalin arzikin Sin da Amurka suka kawo, don more kyakkyawar manufa wajen yin gyare-gyare da raya kasashen biyu, da kokarin neman fifikon kasashensu, don inganta hadin gwiwa a fannonin cinikayya, zuba jari, da aikin gona, da sadarwa, da kira motoci, da kiyaye muhalli a tsakaninsu, kana ya kamata a bada muhimmanci game da musayar al'adu a tsakaninsu, don yalwata hadin gwiwa ta fuskokin ilmi, da yawon shakatawa, da wasanni, da matasa a tsakaninsu, da nufin bude sabon babi na hadin gwiwa a tsakanin kasashen biyu. (Bako)