A yayin da yake amsa tambaya dangane da bankin AIIB, da kyautata tsarin kulawa da duniya da sauransu, shugaba Xi ya bayyana cewa, dukkanin kasashen duniya ne suke sa hannun aikin kyautata tsarin kulawa da duniya, tare da cin gajiyarsa. Har kullum Sin tana tsayawa tsayin daka kan ba da gudummawa ga kafa tsarin duniya mai kyau, tare da amincewa da ba da kariya ga wannan tsari a karkashin jagorancin MDD.
A cikin 'yan shekaru sama da 10 da suka wuce, yayin da take samun ci gaba, Sin ta ci gajiyar hadin gwiwa sosai da sauran kasashen duniya. A sabili da haka, dole ne Sin ta ba da gudummawa ga samun ci gaban duniya.
A yayin da yake amsa tambayar da ta shafi manufofi da matsayin da Sin ta dauka yayin daidaita batutuwan shiyya shiyya da na duniya, shugaba Xi ya jaddada cewa, Sin tana tsayawa tsayin daka kan manufar demokuradiyya irinta neman yancin kai ba tare da tsangwama ba, tana son yin kokarin tabbatar da zaman lafiya da ci gaba a duniya. Yanzu Sin ba za ta sami ci gaba ita kadai ba, ba za ta sami babbar moriya ba sai dai duk kasashen duniya sun sami ci gaba. Sin ta ba da gudummawa sosai a fannonin sa kaimi ga farfado da tattalin arzikin duniya, da daidaita harkokin shiyya shiyya da na duniya a siyasance, da tinkarar matsalolin duniya da kalubaloli iri iri. Wannan ne burin kasashen duniya, kuma alhaki ne na kasar Sin.
Sin da Amurka, zaunannun membobi ne na kwamitin sulhu na MDD, wadanda suka dauki babban nauyi dake wuyansu na tabbatar da zaman lafiya da tsaro a shiyya shiyya har ma a duniya baki daya, tare da moriyar iri daya. A sabili da haka, Sin na fatan tinkarar manyan batutuwan shiyya shiyya da na duniya tare da kasar Amurka.(Fatima)