in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ganawa tsakanin shugabannin Sin da Amurka za ta ciyar da hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu gaba, in ji masanin Amurka
2015-09-21 14:16:53 cri

Kwanakin baya, shahararren masanin kasar Amurka kan batun kasar Sin Kenneth Lieberthal ya gaya wa manema labarai cewa, ganawar da shugabannin kasashen Sin da Amurka wato Xi Jinping da Barack Obama za su yi za ta kara ciyar da hadin gwiwa tsakanin kasashen nan biyu gaba.

Masanin ya ce, kasashen biyu na kokarin kyautata huldar da ke tsakaninsu domin ganin an daidaita manyan matsalolin kasa da kasa da na shiyya-shiyya da ake fuskanta, ganawar da za su yi za ta samar da damar yin cudanya mai zurfi gare su, hakan yana da muhimmanci sosai ga bunkasuwar dangantakar kasashen biyu. Lieberthal yana fatan Sin da Amurka za su ci gaba da gudanar da hadin gwiwa yadda ya kamata, ko da yake ya kasance sabane-sabane da rigingimu tsakaninsu, da yadda za su samu moriya tare.

Game da hakikanin sakamakon da za a samu yayin ganawar, Lieberthal ya ce, kila sassan biyu za su sanar da tsare-tsare da dama domin kara karfafa farhimtar juna tsakaninsu.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China