in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bar birnin Beijing don kai ziyara kasar Amurka
2015-09-22 14:32:00 cri

A yammacin yau Talata ne, bisa goron gayyatar shugaban kasar Amurka Barack Obama, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bar birnin Beijing, don kai ziyara kasar Amurka. Kazalika, bisa goron gayyatar sakatare janar na M.D.D. Ban Ki-Moon, shugaba Xi zai ziyarci hedkwatar M.D.D. dake birnin New York, don halartar taron koli na cika shekaru 70 da kafa M.D.D.

Daga cikin wadanda suka rafa wa shugaba Xi baya a wannan ziyara, sun hada da mai dakinsa Madam Peng Liyuan, da mamban ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin kuma direktan sashen nazarin manufofi na kwamitin tsakiya Wang Huning, da mamban ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na jam'iyyar, kuma sakatare na ofishin kula da kwamitin tsakiya, kana direktan ofishin kula da harkokin yau da kullum na kwamitin tsakiya Li Zhanshu da mamban majalisar gudanarwar kasar Yang Jiechi.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China