in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya gana da shugaban hukumar zartaswar News Corporation
2015-09-18 21:29:36 cri
A yau Juma'a a ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da shugaban hukumar zartaswar News Corporation ta kasar Amurka.

A yayin ganawar shugaba Xi ya bayyana cewa, kasashen Sin da Amurka manyan kasashe ne a duniya, wannan ya sa shi da shugaba Obama na kasar Amurka suka cimma wani muhimmin ra'ayi wato kafa sabuwar dangantakar dake tsakanin manyan kasashen biyu, wadda ba tsokanan juna da girmama juna, da hadin kai don cimma nasara tare, wato dangantakar da ke dacewa da moriyar bai daya ta kasashen biyu.

Xi ya nuna cewa, bisa gayyatar da shugaba Obama ya yi masa zai kai ziyarar Amurka nan ba da dadewa ba, ziyarar da ke da nufin karfafa hadin kai a fannoni daban daban tsakanin kasashen biyu, da kuma zurfafa zumunta tsakanin jama'ar kasashen biyu, ta yadda za a inganta bunkasuwar dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka.

Kazalika shugaba Xi ya bayyana cewa, kasar Sin za ta ci gaba da bude kofa ga kafofin watsa labaru na kasashen ketare, kuma tana yi musu maraba da zuwa nan kasar Sin, don bayanawa duniya yadda bunkasuwar kasar Sin take.

A nasa bangaren, Modoch ya bayyana cewa, kafofin watsa labaru na Amurka da na duniya baki daya suna mayar da hankali kan ziyarar aiki da shugaba Xi zai kai a Amurka. Yana mai cewa, dangantakar dake tsakanin kasashen Sin da Amurka na da muhimmanci kwarai, kuma suna ta kara samun moriyar bai daya, hakan ya kasance muhimmin abu wajen tabbatar da bunkasuwar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China