Ministan harkokin waje na kasar Sin ya yi musayar ra'ayi tare da takwaransa na Amurka
A yau Litinin, ministan harkokin waje na kasar Sin Wang Yi ya yi musayar ra'ayi tare da takwaransa na kasar Amurka John Kerry ta wayar tarho, inda Mr.Wang Yi ya ce, bisa goron gayyatar shugaba Obama, shugaban kasar Sin Xi Jinping zai kai ziyarar aiki kasar Amurka daga ranar 22 ga wata, ziyarar da ke jawo hankalin duniya, wadda kuma ke da matukar muhimmanci ga huldar da ke tsakanin kasashen biyu da ma yanayin da duniya ke ciki.
A nasa bangare, Mr.Kerry ya ce, Amurka na farin ciki da ziyarar da shugaba Xi Jinping zai kawo, kuma tana shirye-shiryen da za su tabbatar da nasarar wannan ziyara, ta yadda za a kara ciyar da huldar kasashen biyu gaba.(Lubabatu)