Mai ba da taimako ga ministan harkokin waje na kasar Sin Mr. Zheng Zeguang ya ce, ta wannan ziyara, ba kawai bangarorin biyu za su iya zurfafa hadin gwiwarsu ta fannonin ciniki da aikin soja da makamashi da kiyaye muhalli da zirga-zirgar sararin sama ba, har ma za su kai ga kara daidaitawa da juna a fannonin bunkasuwar tattalin arzikin duniya da sauyin yanayi da kiyaye zaman lafiya, tare kuma da cimma daidaito a kan batutuwan da suka shafi yankin Asiya da tekun Pasifik da batun nukiliyar kasar Iran da na zirin Koriya da ma batun Afghanistan da sauran harkokin shiyya shiyya. (Lubabatu)