Mataimakin zaunannen wakilin Sin a MDD, Wang Min ya bayyana bayan kada kuri'a cewa, jigilar kananan makamai da na marasa nauyi ba bisa doka ba ta tsanantar da rikice-rikice a shiyya shiyya, da kawo tabarbarewar yanayin da ake ciki, da taimakawa bunkasuwar ta'addanci da laifuffuka da aka aikata tsakanin kasashe da dama, da haka za ta haddasa mutuwa da kuma jikkatar farare hula. Gwamnatin Sin tana tsayawa tsayin daka kan yaki da jigilar irin wadannan makamai ba bisa doka ba. Kamata ya yi kwamitin sulhun MDD ya kara taka rawar a zo a gani, domin kara kokarin shawo kan wannan batu yadda ya kamata.
A sa'i daya, Wang ya ce, a yayin taron, wasu kasashe, musamman ma kasashe uku na Afirka sun fitar da wasu muhimman shawarwarin da suka dace. Kamata ya yi a saurara tare da yin la'akari da wadannan shawarwari, a kokarin neman wata hanyar da ta dace wajen daidaita wannan batu. Amma ba a gudanar da aiki ta wannan hanya ba, lallai ana bakin ciki sosai.
Sin da Angola da Chadi da Nijeriya da Rasha da kuma Venezuela sun jefa kuri'ar janye jiki a yayin taron.(Fatima)