in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane sama da 10 sun mutu sakamakon zanga-zangar da aka yi a hedkwatar Burkina Faso
2015-09-20 14:14:20 cri
A jiya Asabar 19 ga wata, babban kwamandan rundunar sojan kasar Burkina Faso ya tabbatar da cewa, zanga-zangar da aka yi domin yin allawadai da juyin mulkin soja a birnin Ouagadougou, hedkwatar kasar, ta riga ta haddasa mutuwar mutane sama da 10, yayin da mutane sama da dari daya suka jikkata.

A cikin sanarwar, babban kwamandan ya yi Allah wadai da danyun ayyukan da aka yi wa fararen hula, ya ce, alhakin sojojin kasa shi ne ba da kariya da tsaron lafiyar jama'a da dukiyoyinsu. A sabili da haka, ya yi kira ga jama'ar kasar da su tabbatar da kwarin gwiwarsu kan samun wani shirin daidaita wannan batu cikin lumana bisa kokarin bangarori daban daban.

Tun daga ranar 16 ga wata zuwa yanzu, mutane da yawa suka cigaba da nuna adawa da juyin mulkin soja, tare da fitowa a kan titunan birnin Ouagadougou, inda kuma sojojin suka yi kokarin tarwatsa su ta hanyar harbe bindiga, a lokacin da masu zanga-zanga suka jefa musu da duwatsu domin mai da martani. Kawo yanzu, rikicin a birnin Ouagadougou ya haddasa mutuwar mutane sama da 10, yayin da wasu mutane sama da dari daya suka ji rauni.

A ranar 18 ga wata, majalisar tabbatar da zaman lafiya da tsaro ta kungiyar tarayyar kasashen Afrika ta ba da sanarwar cewa, bisa yanayin da ake ciki a yanzu, za ta dakatar da kasar Burkina Faso a matsayin memba ta kungiyar AU kafin da ta sake tabbatar da zaman lafiya a kasar, kuma ta yi barazanar hukunta shugabannin sojojin da suka yi juyin mulkin. Bisa matsin lamba kuma, "hukumar wanzar da dimokuradiyya ta Burkina Faso" ta saki shugaban rikon kwarya, Michel Kafando da ministoci biyu da rundunar tsaron shugaban kasa ta tsare.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China