A cewar 'yan majalisun, wannan wata dama ce ta cike gibin shari'a a wannan fanni. A cewar wannan sabuwar doka, duk mutanen da aka tabbatar da aikata wadannan laifuka na cin zarafin mata, za'a yanke musu hukuncin zaman yari har na zuwa shekaru biyar da cin su tara ta kusan Sefa jika dari shida zuwa miliyan 1,5 kimanin dalar Amurka dubu guda zuwa dubu biyu da dari biyar, ko kuma daya daga cikin wadannan hukunce hukunce biyu kawai. (Maman Ada)