Yanzu dai Michel Kafando ne zai maye gurbin Laftan kanar Yacouba Isaac Zida wanda ya karbi mulki a hannun Blaise Compaore wanda boren al'ummar kasar ya tilasta masa sauka daga karagar mulki.
An haifi Michel Kafando ne a ranar 18 ga watan Agusta na shekarar 1942, kuma ya rike mukamai da dama da suka hada da ministan harkokin wajen kasar da kuma wakilin kasar Burkina Faso a MDD.
Kungiyoyin fararen hula da jam'iyyun siyasa da wakilan sojojin kasar ne suka zabi jami'in cikin sunayen mutanen da aka gabatar musu.
Ya kuma yi alkawarin kafa gwamnatin rikon kwarya bisa tsarin dimokuradiya cikin gaskiya da adalci.
A ranar Talata da safe, agogon kasar Burkina Faso ne za a rantsar da Michel Kafando a matsayin mutumin da zai jagoranci kasar har zuwa watan Nuwamban shekarar 2015, lokacin da za a gudanar da zaben 'yan majalisu da na shugaban kasa. (Ibrahim)