A wani ci gaban kuma, shugaban karba-karba na kungiyar tarayyar tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ta (ECOWAS), kuma shugaban kasar Senegal Macky Sall, tare da shugaban kasar Benin Boni Yayi sun tashi zuwa birnin Ougadougou, domin fara aikin shiga tsakani, game da rikicin kasar ta Burkina Faso.
A ranar Larabar da ta gabata ne rundunar tsaron shugaban kasar Burkina Faso dake biyayya ga tsohon shugaban kasar, ta cafke shugaba da firaministan wucin gadin kasar, tare da wasu ministoci biyu na gwamnatin. A kuma ranar Alhamis rundunar ta sanar da karbe madafan ikon kasar, tare da hambarar da shugaban wucin gadin kasar, tare da rushe gwamnatin wucin gadin.
Har wa yau, rundunar ta kuma sanar da kafa majalissar wanzar da dimokaradiyyar kasar a matsayin hukumar kolin kasar. (Lubabatu)