Daga nan sai ya yi kira ga dakarun da suka aiwatar da juyin mulkin da su martaba kudurin mika mulki ga halastacciyar gwamnati, ta hanyar gudanar da sahihin zabe.
Bisa shirin gudanar da babban zaben kasar a ranar 11 ga wata mai zuwa, tuni Najeriyar ta gabatar da tallafin motoci kirare a-kori-kura guda 20, ga hukumar zaben kasar ta Burkina Faso.
Shugaba Buhari ya kuma yaba da sakin shugaban rikon kwaryar kasar Michel Kafando, yana mai kira da a saki sauran kusoshin gwamnatin rikon kwaryar kasar, da suka hada da firaminista Isaac Zida. Ya ce Najeriya za ta ci gaba da goyon bayan kungiyar ECOWAS a shirinta na shiga tsakani a rikicin siyasar Burkina Fason, shirin da shugaba Macky Sall na Senegal, da takwaransa na Benin Boni Yayi ke jagoranta. (Saminu Hassan)