Kwamitin sulhu na MDD ya yi kira ga bangarori daban daban na kasar Burkina Faso da su nuna goyon baya ga gwamnatin rikon kwarya
2014-11-18 15:13:40
cri
Kwamitin sulhu na MDD ya bayar da wata sanarwa a ranar 17 ga wata, inda ya yi maraba da yarjejeniyar da aka daddale game da tsarin mulkin wucin gadi na kasar Burkina Faso da kuma zaben shugaban wucin gadi da zai jagoranci wannan kasa dake yammacin nahiyar Afrika. Haka kuma kwamitin ya yi kira ga bangarori daban daban na kasar da su samar da hadin kai ga hukumomin gwamnatin wucin gadi na kasar ta yadda za su samu zarafin gudanar da ayyukansu yadda ya kamata. (Zainab)