Zamanin juyin mulki ya wuce amma ya dawo. Babu wani dalilin yin amfani da karfin sojoji domin kai samun mulki a Afrika, in ji wata sanarwar da ta fitar a shafinta na internet.
Bisa matsayinta na nacewa wajen saukaka da gina shawarwari, African Crisis Group na hada kai da gamayyar kasa da kasa da kuma daukacin kungiyoyi masu imani da adalci da zaman lafiya a kasar Burkina Faso domin aiwatar da wani shirin gaggawa da lumana domin dawowar tsarin mulkin, in ji African Crisis Group dake cibiya a Ouagadougou da Conakry, wadda muhimmin aikinta shi ne na gina da karfafa zaman lafiya a Afrika.
A ranar Jumma'a da yamma, shugaban Senegal Macky Sall, da takwaransa na Benin Yayi Boni masu shiga tsakani sun gana bi da bi da tawagar 'yan majalisu na kwamitin kasa na kula da rikon kwarya (CNT), da wakilan kungiyoyin fararen hula da kuma shugaban sojojin da ya yi juyin mulki, janar burgediya Gilbert Diendere, tsohon shugaban rundunar sojoji na musammun na tsohon shugaban kasar Blaise Compaore. (Maman Ada)