in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta fitar da ranar kawo karshen fyade a lokutan yaki
2015-06-20 14:12:30 cri
Babban zauren MDD a ranar Jumma'ar nan ta amince da shawarar kebe ranar musamman ta kawo karshen cin zarafi a lokutan yaki a kowace ranar 19 ga watan Yuni, a wani mataki na kara matsa lamba a duniya baki daya a yaki wannan tashin hankali da mata da 'yan mata suke fuskanta a yankunan da ake yaki.

Sabuwar dokar ta babban zauren majalissar kasashe 113 ne suka gabatar da bukatar shi na ganin an tsaida mashi rana ta musamman wanda yanzu a duk shekara za'a kebe shi domin wayar da kan jama'a na bukatar kawo karshen cin zarafin mata da 'yan mata da ake yi a lokacin rikici tare da kira ga daukacin kasashen duniya da su tashi tsaye don bada goyon bayansu da hadin kai ga wadanda suka tsira daga wannan masifa a duk fadin duniya.

Wannan rana, sai dai ta zo ne sakamakon rahotannin da suka fito wadanda ke bayyana irin mugun cin zarafin da mata da 'yan mata ke fuskanta a hannun wadannan 'yan kungiyar ta'addanci masu alaka da IS.

Rahotannin baya bayan nan da MDD ta fitar akan cin zarafin dake da alaka da yake yake ya bayyana irin tashin hankalin da 'yan mata ke fuskanta da suka hada da fyade na wulakanci, bautar da su don cin zarafin su kawai da kuma auren dole a kasashen da suka hada da jamhuriyar afrika ta tsakiya,Iraqi,Somaliya,Sudan, Sudan ta kudu da kuma Syria.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China