MDD ta kaddamar a ranar Laraba, a birnin Pretoria, hedkwatar kasar Afrika ta Kudu, da wani shirin kai da kawo na ba da horo ga mata masu kamfanoni.
Shirin mai taken "iLearn" na daya daga cikin ayyukan daga tushe na kyauta kan shafin yanar gizo, in ji MDD-Mata, wata cibiyar da babban taron MDD ya kafa domin tabbatar da daidaici tsakanin jinsuna da samar wa mata 'yancin gudanar da harkokinsu da kansu.
Shirin iLearn, da aka kaddamar a Pretoria, na samar da wani dandali inda mata masu kamfanoni ke bayyana tarihinsu bisa lafazinsu da kuma raba kwarewarsu da sauran mata. (Maman Ada)