in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD za ta hada gwiwa da Sin don kara inganta rayuwar mata a Afirka
2015-06-15 09:26:51 cri

Babbar jami'ar hukumar kula da harkokin mata ta MDD Phumzile Mlambo-Ngcuka ta ce, hukumarta na shirin hada gwiwa da kasar Sin, ta yadda za a kara ilimantar da mata game da harkokin zuba jari a nahiyar Afirka.

Madam Phumzile Mlambo-Ngcuka ta yi wannan tsokaci ne a taron kolin kungiyar kasashen Afirka ta AU karo na 25 mai taken samar da 'yanci ga mata da ke gudana a Afirka ta kudu.

Mataimakiyar babban magatakardar MDDr ta kara da cewa, kasar Sin da hukumarta za su shirya wani taron kolin mata na duniya a watan Satumban wannan shekara a daidai lokacin da ake bikin cika shekaru 20 da shirya taron kolin mata na birnin Beijing na shekarar 1995, taron da ya fito da wani kundin mai muhimmanci kan kare 'yancin mata.

Ta yi fatan cewa, kasar Sin za ta yi amfani da wannan dama wajen zuba jari a nahiyar Afirka, musammnan jarin da zai yi kyakkyawan tasiri ga rayuwar mata. Kasar Sin dai na daga cikin kasashe kalilan da suka zuba jari a nahiyar ta Afirka, musamman a bangaren ababan more rayuwa da nufin bunkasa tattalin arzikin nahiyar.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China