Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi shawarwari tare da shugaban kasar Mauritania Mohamed Ould Abdel Aziz a jiya Litinin 14 ga wata a babban dakin taron jama'a dake nan birnin Beijing, inda shugabannin biyu suka amince da tsara shirin raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu da kara inganta hadin gwiwarsu.
Xi Jinping a jawabin shi ya yi maraba da zuwan Mohammed Ould Abdel Aziz kasar Sin don halartar bikin baje koli na Sin da kasashen Larabawa na shekarar 2015. Haka kuma Mr Xi ya yi nuni da cewa, Sin ta nuna godiya ga kasar Mauritania da ta nuna goyon baya gare ta kan manyan batutuwan dake shafar moriyar kasar Sin,kuma za ta ci gaba da nuna goyon baya ga kasar Mauritania don ta kiyaye zama lafiya da samun bunkasuwa.
Xi Jinping ya jaddada cewa, Sin tana son yin mu'amala tare da membobin dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka ciki har da kasar Mauritania, kana za ta maida taron ministoci karo na shida na dandalin tattaunawar da za a yi a kasar Afirka ta Kudu a shekarar badi a matsayin gagarumin taro na kara hada kai da samun moriyar juna a tsakanin Sin da Afirka. Hakazalika kuma, Sin tana son kara yin hadin gwiwa a tsakaninta da kasar Mauritania bisa tsarin dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa a tsakanin Sin da kasashen Larabawa.
A nasa bangare, shugaba Mohammed Ould Abdel Aziz ya bayyana cewa, kasar Mauritania tana son kara yin mu'amala tare da kasar Sin kan harkokin kasa da kasa, da taka rawarta a taron dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka. (Zainab)