Shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya bukaci hukumar zurfafa yin gyare-gyare ta kasar da ta kara bude kafofin tattalin arzikin kasar ga sassan duniya a wani mataki na za a kara bunkasa tattalin arzikin kasar.
Shugaba Xi wanda ya bayyana hakan yayin taron babban kwamitin zurfafa gyare-gyare na kasa karo na 16 ya ce, kamata ya yi kasar Sin ta kara kokarin janyo hankulan masu sha'awar zuba jari da fasahohi daga ketare tare da kara inganta matakan bude kofa ga kasashen waje.
Shugaba Xi ya ce, matakan da ake dauka na kara bude kofa yayin da ake zurafa yin gyare-gyare a kasa za su kara bunkasa tattalin arzikin kasa.
A baya dai hukumar zurfafa yin gyare-gyare ta bullo da dokoki da suka hada da na daidaita harkokin kasuwanni, manufofin da suka shafi tsaron kan iyaka, karfafawa masana'ntun gwamnati karbar jari daga sassa masu zaman kansu, baiwa baki takardun iznin zaman duk da nufin bunkasa tattalin arzkin kasar.(Ibrahim)