A yayin ganawar, Xi Jinping ya nuna cewa, bangaren Sin yana kokarin bunkasa hadin gwiwar moriyar juna ta sada zumunta tsakanin kasashen biyu daga dukkan fannoni. Ya ce ya kamata kasashen biyu su hanzarta tuntubar juna, ta yadda za a iya tabbatar da aiwatar da abubuwa daban daban bisa babbar manufar hadin gwiwa da kasashen biyu suka tsara, kuma za a iya mayar da matsaya daya da shugabannin kasashen biyu suka cimma da ya zama sakamakon hadin gwiwa da zai amfanawa jama'ar su.
Bugu da kari, Shugaba Xi Jinping ya jaddada cewa, kasar Sin na son ci gaba da kara daidaita tare da goyon baya da kasar Afirka ta kudu kan harkokin da ya shafi bangarori daban daban domin kare hakkin kasashe masu tasowa tare. Kuma za ta hada kan kasashen Afirka kan aikin shirya taron kolin dandalin hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka da za a yi a kasar Afirka ta kudu a watan Disamba na wannan shekarar.
A nasa bangaren, Mr. Jacob Zuma ya bayyana cewa, kasarsa na mai da hankali kan huldar sada zumunta dake tsakanin kasarsa da kasar Sin, kuma zai yi kokarin mayar da babbar manufar hadin gwiwa da kasashen Afirka ta kudu da Sin suka tsara tare da ta zama sakamakon da ake fata. Har ila yau Shugaba Zuma ya ce, kasar Afirka ta kudu za ta yi hadin gwiwa da kasar Sin domin kokarin samun nasarar shirya taron koli na dandalin hadin gwiwar kasashen Afirka da Sin. (Sanusi Chen)