Wang Yi ya bayyana cewa yayin ziyarar, shugaba Xi zai mayar da hankali wajen karfafa fahimtar juna tare da kawar da shakkun da Amurkan ke da shi game da yadda bangarorin biyu ke yi wa juna bahaguwar fahimta kan al'amuran kasa da kasa da batutuwan da suka shafi yankin Asiya da fasifik.
Bugu da kari, ana sa ran shugabannin biyu su cimma yarjejeniya a fannonin da suka shafi harkokin kudi da cinikayya, makamashi, batun sauyin yanayi da kiyaye muhalli. Sauran sassan sun hada da kimiya da fasahar kere-kere, aikin gona, martaba doka, harkokin jiragen sama da kuma kayayyakin more rayuwa.
Ministan Wang Yi ya jaddada cewa, kasashen biyu suna da albarkatu da kuma damammakin da za su cimma nasarori da hadin gwiwar da ta dace game da yankin Asiya da facifik.
A yayin ziyarar ce kuma ake fatan sanar da jerin matakan inganta musaya tsakanin al'ummomin kasashen biyu. (Ibrahim)